An yi zaman ta'aziyar, dangin marigayin tare da manyan jami'an gwamnatin Iran da suka hada da shugaban kasa da kuma shugaban majalisar dokoki gami da babban alkalin alkalai, gami da sauran dubban mutane daga ko'ina da suke halartar wurin.
A farkon zaman dai an bude wurin da karatun kur'ani mai tsarki, da kuma karato wasu daga cikin bayanai na manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka.
A jiya ne dai aka gudanar da janazar Ayatullah Hashimi rafsanjani, wanda jagoran juyin juya halin muslunci Ayatullah Sayyid Ali Khamunai ya jagoranta, an kuma bizne gawar tasa ne a cikin hubbaren marigayi Imam Khumaini (R.A) da ke kudancin birnin Tehran.288